IlimiUncategorized

Gwamnatin Kano Za Ta Kashe Sama Da Miliyan 79 Wajen Farfaɗo Da Makarantun Kwana

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewar, Gwamnatinsa za ta kashe kimanin Naira 79,284,537 wajen sake farfaɗo da wasu Makarantun Kwanan Jihar guda 11.

Gwamnan ya bayyana haka ne, a yau (Juma’a) ta shafinsa na Facebook, inda ya ce hakan ya biyo bayan amincewa da batun da aka yi ne, a zaman majalissar zartarwa na biyar, da ya Jagoranta, a jiya.

Waɗannan maƙudan kuɗaɗe kuma, wani sashe ne daga cikin, Naira 4,882,378,071 da Gwamnatin ta ware, wajen gudanar da wasu muhimman ayyuka, a jihar ta Kano.

“Taron Majalissar Zartarwar Kano na 5, wanda na Jagoranta a jiya, ya amince da kashe kimanin Naira 79,284,537 wajen farfaɗo da Makarantun Kwanan da aka yi watsi da su guda 11, a Jihar nan.

“Wannan kuma, wani ɓangare ne, daga kimanin Naira 4,882,378,071 da aka saki, domin gudanar da muhimman ayyuka da dama, a wannan Jiha. – AKY”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button