Zamantakewa

Gwamnatin Katsina Ta Tuɓe Rawanin Hakimi, Bayan Ɗaura Aure Ba Tare Da Gwajin Lafiya Ba

Gwamnatin jihar Katsina, ta sauke Hakimin Kuraye, Alhaji Abubakar Abdullahi-Ahmadu, daga kan Sarautarsa.

Wani jawabi da, Alhaji Abdullahi Aliyu-Yar’adua, da ke zama Daraktan al’amuran yaɗa labarai na Gwamnatin ya fitar, ya bayyana cewar, Gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne, bayan buƙatar hakan da Majalissar Masarautar Katsina da shigar mata.

“An karɓi ƙorafi akansa, Kuma majalissar Masarauta ta bincika lamarin.

“An kuma samu Abdullahi-Ahmadu da laifin ɗaura Aure ba tare da buƙatar gabatar da takardar shaidar gwajin lafiya (Medical Certificate) ba, kamar yadda doka ta tanada.

“Kuma an samu guda daga cikin Ma’auratan da ciwon Sida (ƙanjamau/HIV), Wanda kuma hakan ya biyo bayan laifin Hakimin ne, wanda ya ɗaura Auren, ba tare da gwajin lafiya ba”., A cewar jawabin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button