Wasanni

Gwamnatin Lagos Ta Samar Da Cibiyoyin Kallon Ƙwallo 25, Gabanin Wasan Najeriya Da Bafana-Bafana

Gabanin wasan da za a fafata tsakanin tawagar kwallon kafar kasa Najeriya ta Super Eagles da Afirka ta kudu, yau Laraba a wasan kusa da na karshe na gasar Kofin kasashen Afirka, Gwamnatin jihar Lagos, ta samar da Cibiyar kallon kwallo ta musamman, a filin wasa Mobolaji Johnson, da ke yankin Onikan.

Babbar cibiyar kallon kwallon kuma, guda ce cikin 25 da Gwamnatin ta samar a jihar, domin bunkasa walwalar alúmmar jihar da ke da shaáwar bibiyar alámuran kwallon kafa, tun bayan fara wasan a ranar 13 ga watan Janairun da ya gabata, a kasar Cote’Dívoire.

Wasan da za a fafata tsakanin Super Eagles da Bafana Bafana, a yau din kuma, shi ne karo na hudu da tawagogin biyu su ka taba haduwa, inda Eagles din ta kasa Najeriya ta lashe dukkannin wasanni ukun da su ka kece raini a baya.

Ta cikin wani jawabi da ya fitar, a ranar Talata, Kwamishinan yada labaran jihar ta Lagos, Gbenga Omotoso, ya bayyana cewar, yana da matukar muhimmanci magoya bayan tawagar kwallon kafar ta Najeriya su kasance da wasan kaitsaye, kasancewar jihar ta Lagos babbar magoyiyar bayan tawagar Najeriya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button