Gwamnatin Nasarawa Ta Nisanta Kanta Da Rundunar Fulani
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nisanta gwamnatin jihar, da rundunar tsaron Vigilante ta Fulanin jihar.
Gwamnan, ya nisanta gwamatin da wannan batu ne, ranar Litinin, a birnin Lafia, ya yin da membobin majalissar dokokin jihar, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Hon. Danladi Jatau, su ka kai masa ziyarar taya murna, kan nasarar da ya samu a Kotun Ƙoli.
Gwamnan ya ce, jihar ba ta zaɓi rundunar tsaron Vigilante ɗin Fulanin ba, kamar yadda babu wata ƙungiyar tsaro da ta zame mata shalele.
Ya kuma ce, da Gwamnatin jihar na da hannu cikin lamarin, da za ta aike da ƙudirin dokar samar da rundunar ga majalissa, a hukumance.
A.A. Sule, ya kuma ce, Gwamnatin jihar, za ta cigaba da tsayawa kai da fata wajen ganin zaman lafiya ya tabbata a jihar, ya na mai umaryar hukumomin tsaro da su bincike lamarin samar da rundunar tsaron Fulanin.
Bugu da ƙari, Gwamnan ya ce, a matsayinsa na mai muradin ganin ɗorewar zaman lafiya, sam ba zai ƙarfafi gwuiwar wanzar da rashin tsaro a jihar ta Nasarawa ba.
A nasa ɓangaren, Shugaban ƙungiyar Fulani ta ƙasa, Abdullahi Badejo, ya ce samar da rundunar tsaron da ta sa kai, zai ƙara ƙarfafa tsaro ne a Najeriya, kuma rundunar za ta dinga gudanar da ayyukanta ne, dai-dai da tanadin dokokin ƙasa.
Ya na mai cewar, manufar farko ta samar da rundunar, shi ne magance matsalolin tsaro, kamar ayyukan ƴan bindiga, garkuwa da mutane, da ma satar shanu, a jihar ta Nasarawa.