Tsaro
Gwamnatin Nasarawa Ta Sha Alwashin Bunƙasa Al’amuran Tsaron Jihar
Da safiyar Talata ne, kwamishinan Shari’a, kuma Atoni Janar na jihar Nasarawa, Barista Magaji, ya gabatar da muƙala mai taken ‘Rawar Da Ya Kamata Hukumomin Tsaro Su Taka Wajen Tabbatar Da Ɗorewar Tsaro Da Zaman Lafiya A Jihar Nasarawa’.
Kwamishinan ya kuma gabatar da wannan jawabi ne, a ya yin da tawagar Ɗaliban Kwalejin Horas Da Jami’an Tsaro, da ke Jaji, aji na 46, su ka kai masa ziyara.
Haka ma dai, da safiyar Talatar ne, Kwamishinan Shari’ar, ya ziyarci Kotun Ƙolin Najeriya, da ke babban birnin tarayya Abuja, domin wakiltar, Gwamna Abdullahi A. Sule, a taron ɗaga likkafar wasu Lauyoyi zuwa muƙamin ƙololuwa na SAN.