Gwamnatin Tarayya Ƙaddamar Da Shafin Rijistar Ƙananan Kamfanonin Fasaha
Gwamnatin tarayya ta sanar da ƙaddamar da shafin tallafawa ƙananan kamfanonin fasaha (startups).
Shafin, wanda guda ne daga cikin manyan ababen da ake buƙata domin ƙaddamar da dokar ƙananan kamfanonin fasahar, gwamnati ta samar da shi ne da nufin kasancewa kafar da za ta dinga tantance ƙananan kamfanonin a ƙasar nan.
Ministan sadarwa, da bunƙasa tattalin arziƙin zamani, Dr Bosun Tijani, shi ne ya bayyana hakan, a daren jiya, ta shafinsa na kafar sada zumunta ta X.
Ta cikin saƙon nasa, Ministan ya bayyana samar da shafin mai adireshin https://startup.gov.ng/, a matsayin babban abin da ake buƙata, kafin ƙaddamar da dokar ƙananan kamfanonin fasaha na ƙasa.
Ya kuma haska cewar, samar da shafin, wanda zai kasance tamkar wani zaure na tattaunawar ƙananan kamfanonin fasahar, zai bada damar wakilan hukumar bunƙasa dogaro da kai ta fuskar tattalin arziƙin zamani su shiga ciki.