Gwamnatin Tarayya Da Asusun Duniya Za Su Haɗa Gwuiwa Domin Inganta Kiwon Lafiya, A Kano
Gwamnatin tarayya, tare da haɗin guiwar Asusun Duniya (Global Fund), da wasu ɓangarorin bunƙasa cigaba, sun ƙuduri aniyar sake inganta tsarin kiwon lafiyar ƙasar nan.
Ministan lafiya, Dr. Mohammed Ali Pate, shi ne ya bayyana hakan a yau, ya yin da ya jagoranci wakilcin Asusun Duniya, da na sauran ɓangarorin cigaba, zuwa Fadar Gwamnatin jihar Kano.
A ya yin ziyarar dai, an jiyo Ministan ya na bayyana inganta lafiyar al’umma a matsayin babban jigon cigaban kowacce jiha, ya na mai cewa, wajibi ne fannin lafiya ya kasance babban abinda kowacce Gwamnati za ta sanya a gaba.
Ya kuma ce, jihar Kano ce akan gaba ta fuskar yawaitar fama da zazzaɓin cizon sauro (Malaria), inda ya roƙi Gwamnatin Kanon da ta sake zage damtse wajen ganin ta sake bunƙasa fannin lafiyarta.
A nasa ɓangaren, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce Kano na cigaba da kasancewa a gaba-gaba a ƙasar nan ta fuskar kiwon lafiya, duk kuwa da fatara, da rashin kuɗin da ake fama da shi a ƙasar, Gwamnati na yin dukkannin bakin ƙoƙarinta wajen fitar da kuɗaɗe dan ganin an samarwa fannin na lafiya abinda ya ke da buƙata.
Da ya ke bayyana farincikinsa kan yadda jihar Kanon ke ƙoƙarin ciyar da fannin lafiyarta gaba, Babban Daraktan Asusun Duniya, Peter Sands, ya sha alwashin bayar da ƙarin gudunmawa da goyon baya, wajen cigaban fannin, a jihar Kano.