Labarai
Gwamnatin Tarayya Za Ta Ɗebo Al’ummar Najeriya Da Ke Maƙale A Sudan, Ta Tituna
Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ya bayyana cewar, hanya guda da ta rage ta dawo da al’ummar ƙasar nan da su ke cigaba da ɓuya a Sudan, sakamakon yaƙi, ita ce ta titi.
Onyeama ya kuma bayyana hakan ne ranar Lahadi, a tashar Talabijin ta Channels, cikin shirin siyasa na Politics.
A cewar ministan dai, filayen sauka da tashin jiragen sama sun fi ƙarfin hukumar a yanzu, sakamakon yaƙin da ake cigaba da tafkawa, a tsakanin babban kwamandan rundunar sojin ƙasar ta Sudan, da ƙungiyar masu ta da zaune tsaye, da ma Jami’an RSF.
Rikicin wanda ke cigaba da gudana a yanzu kuma, ya samu tsoma bakin ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afirka ta AU.