Gwamnatin Tinubu, Ta Wucin Gadi Ce – A Cewar Atiku
Ɗan takarar shugabancin ƙasa, na jam’iyyar PDP, a babban zaɓen 2023 da ya gabata, Atiku Abubakar, ya ce, ya na da tabbacin zai samu nasara akan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a shari’ar zaɓen da su ke fafatawa, yanzu haka, a gaban kotu.
Inda Atikun ya bayyana Gwamnatin ta Bola Tinubu, a matsayin Gwamnatin ‘wucin gadi’, ya na mai ƙarawa da bayyana yadda aka kafata, ta hanyar yi wa dokokin zaɓe karantsaye.
Tsohon Mataimakin shugaban ƙasar, ya kuma bayyana hakane, a ya yin taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar PDP, da aka zaɓa, a jihar Bauchi, ranar Asabar.
A ya yin zaman tattaunar kuma, PDP ta roƙi membobinta da ke majalissun tarayya, da kada su kasance ƴan amshin shata.
Inda Atikun ke bayyana musu cewar, ”Kuna majalissa ne, domin ku yi aiki a matsayin ƴan adawar wannan Gwamnatin ta wucin gadi.
”Idan mu ka yi duba da sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar, da kuma ƙalubalantar zaɓuɓɓukan da mu ke yi a gaban kotu, za mu ga cewar membobinmu ba su ne mafi yawa a majalissun tarayya ba.
”Saboda haka, a wannan lokacin, dole ne a dinga ganin ayyukansu a matsayin ƴan adawa”, a cewar sa.