Gwamnatin Zamfara Ta Ayyana Dokar Ta Ɓaci A Fannin Ilimi
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawan, ya ayyana dokar ta ɓaci a fannin Ilimin jihar.
Ta cikin wata tattaunawa da kafafen yaɗa labaran jihar, da ya gudanar a jiya, Gwamnan ya ce halin taɓarɓarewar Ilimin da ke addabar jihar, ya shafi kowanne matakin karatu, tun daga kan Makarantun Firamare, Sakandire, har ya zuwa Manyan Makarantu.
Ya yin da ƙalubalen da makarantun ke fuskanta ya haɗar da: Rashin ingantattun muhallan koyo da koyarwa, da ma rashin wadatattun kayayyakin ayyuka.
Wani jawabi da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya fayyace cewa ayyana dokar ta ɓaci a fannin Ilimin, na daga cikin alƙawurran da Gwamna, Dauda Lawal ya yi wa al’umma, tun a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Jawabin ya kuma ƙara da bayyana cewar, gwamnatin jihar na yin iya bakin ƙoƙarinta wajen bunƙasa fannin Ilimi, wanda a bayyana ta ke cewar, ya na cikin halin ni ƴasu.