Gwamnatin Zamfara Ta Buƙaci Tsohon Gwamnan Jihar, Ya Dawo Da Motocin Da Ya Yi Awon Gaba Da Su
Gwamnatin jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin Gwamna, Dauda Lawal, ta bawa tsohon Gwamnan jihar, Muhammad Bello Matawalle, wa’adin kwanaki biyar domin mayar da wasu motocin alfarma da gwamnatin tace yayi awon gaba da su.
Tunda fari dai, sabuwar Gwamnatin ta zargi cewa, ba ta tarar da komai a fadar gwamnatin jihar ba, domin hatta Murahun girki sai da tsohon gwamnan ya tafi da su.
Irin wannan dambarwa, da ake samu tsakanin sababbi da tsofaffin Gwamnoni musamman idan basu fito daga jam’iyya guda ba dai, na cigaba da kasancewa babban ƙalubalen da Demokradiyyar ƙasar nan ke fuskanta.
Inda ko a jihar Kano ma, rahotanni su ka bayyana yadda sabon Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya ke ta rushe-rushen wuraren da ya ke zargin Gwamnatin tsohon Gwamnan da ya gabata (Ganduje), ta Cefanar da su, ba bisa ƙa’idaba.