Haƙurin Ƴan Ƙasa Ya Kusa Ƙarewa, Kan Makomar Tattalin Arziƙi – SSANU
Shugaban ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i (SSANU), na ƙasa, Mohammed Ibrahim, ya bayyana wa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu cewar, haƙurin al’ummar Najeriya na daf! da ƙarewa.
Ya kuma ce, jama’ar Najeriya su na cigaba da mamakin ta yadda halin matsatsin da aka tsunduma su, zai gyara tattalin arziƙin ƙasar.
Ibrahim, ya bayyana hakan ne, ya yin da ya ke zantawa da Manema Labarai, a wani ɓangare na taron Shiyya na Majalissar zartarwar ƙungiyar karo na 72, da aka gudanar, ranar Juma’a a Jami’ar Ilorin.
Ya kuma ƙara da roƙon Shugaba Tinubu da ya cika alƙawarin da ya ɗauka na ƙara Albashin ma’aikata a zangon farko na shekarar da mu ke ciki.
A nasa jawabin na daban, Mataimakin shugaban ƙungiyar ta SSANU na reshen Yammaci, AbdulSuboor Salam, ya yi Allah-Wadai da halin da tsaro ya tsinci kansa a ƙasar nan, bayan buga misalai da yadda ake ta garkuwa da ma”aikatan Gwamnati a babban birnin tarayya Abuja.
Da ya ke jawabi, a ya yin buɗe taron, ranar Alhamis, Shugaban Jami’ar ta Ilorin, Farfesa Wahab Egbewole (SAN), ya ce gamayyar ƙungiyoyin da ke da rassa a Jami’ar, za su haɗa hannu da hukumar gudanarwarta, domin bunƙasa cigabanta.