Addini

Hajji: An Fara Jigilar Maniyyatan Jihar Kaduna, Zuwa Ƙasa Mai Tsarki

Hukumar kula da jindaɗin Alhazai ta jihar Kaduna, ta fara Aikin kwashe maniyyatan jihar kimanin 6,487, da ake sa ran za su halarci Aikin Hajji a wannan shekarar, zuwa ƙasa mai tsarki.

Da ya ke jawabi, a ya yin tashin jirgin farko na maniyyatan, babban Sakataren hukumar, Dr. Yusuf Arrigasiyyu, ya ce kimanin mutane 390 ne su ka tashi zuwa ƙasar mai tsarki, a karon farko.

Inda ya kuma ce, sun yi dukkannin shirye-shiryen da su ka dace, wajen tabbatar da nasarar jigilar mahajjatan.

Ya kuma ce, sun samar musu da ingantattun wuraren kwana, a tsakanin biranen Makka da Madina, dan tabbatar da sun gudanar da Ibadarsu cikin walwala.

Ka zalika, ya bayyana cewar, hukumar tasu ta gudanar da bita, har ta tsawon makonni 10 ga maniyyatan, dan tabbatar da cewar sun fahimci dukkannin tsare-tsare, da ma dokokin da Ibadar Aikin Hajjin ke da su, ya yin da kuma ya sha alwashin sanya ido kan Mahajjatan dan ganin basu Aikata kura-kurai ba, a ya yin gudanar da wannan Ibada.

Ya kuma ce, jihar za ta yi amfani da jiragen sama na kamfanin Azman Air ne, wajen jigilar maniyyatan.

Ita kuwa, Mataimakiyar Gwamnan jihar, Dr Hadiza Sabuwa Balarabe, roƙar maniyyatan ta yi, da su yi wa jihar, da ma ƙasa baki ɗaya Addu’a, a ya yin gudanar da wannan Ibada tasu mai Albarka.

A nasa jawabin na daban, Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, shawartar maniyyatan ya yi da su kasance masu sanya lura, da taka-tsan-tsan da jakunkunansu, ka da su sake su bawa wasu damar kusantar kayayyakin nasu, ko kuma a basu kaya domin riƙewa, saboda gujewa shiga komar masu safarar miyagun ƙwayoyi.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button