Hajji : Kamfanonin Jiragen Sama Sun Sanya Hannu Kan Yarjejenya Da NAHCON
Hukumar Aikin Hajji ta kasa NAHCON, tare da kamfanonin zirga-zirgar jiragen saman kasar nan guda hudu, da aka amince da su domin jigilar mahajjatan shekarar da mu ke ciki ta 2023, sun sanya hannu kan yarjejeniyar jirgilar mahajjatan, a ranar Talata.
A baya dai, kamfanonin jiragen na kasar nan sun gaza amincewa su sanya hannu kan yarjejeniyar,, bayan da hankalinsu ya karkata kan yakin da ake cigaba da gwabzawa a kasar Sudan, wanda hakan ya sanya basu samu sahalewar ofisoshinsu ba, illla kamfanin jigila na na Saudi Arabian Arilines wanda shi kadaine ya rattaba hannun.
Sai dai, a jiya Talata, manyan jamián kamfanonin sun hallara a ofishin hukumar, tare da rattaba hannun. A jawabinsa, Shugaban hukumar ta NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, godewa himmar kamfonin jigilar ya yi, bisa sadaukarwarsu, duk da irin kalubalen yakin Sudan din da ake fuskanta.