Ilimi

Halin Da Ake Ciki Game Da Alƙawarin Gwamnatin Kano, Na Biya wa Ɗaliban Jami’ar Bayero Kuɗaɗen Makaranta

Hankalin ɗalibai, tare da Iyayen da ƴaƴayensu ke karatu a Jami’ar Bayero, Kano ya tashi, ya yin da wa’adin rufe karɓar kuɗaɗen Makarantar (Registration) ke gab da cika.

Hakan kuma ba ya rasa nasaba da alƙawarin da Gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin Jagorancin, Abba Kabir Yusuf ta yi, na biya wa kimanin Ɗalibai Dubu Bakwai ƴan asalin Jihar, da ke karatu a Jami’ar ta Bayero kuɗaɗen Makaranta. Inda tun daga wancan lokaci, a iya cewa shiru ka ke ji, kamar an aiki bawa garinsu, inda rashin ji daga bakin Gwamnatin ne ma ya sanya ƙungiyar ɗaliban Jihar Kano (NAKSS) ta ɓara kan wannan batu.

Ta cikin wani jawabi da Sakataren kula da al’amuran kuɗi (Financial Secretary), ƙarƙashin Ofishin Kakakin ƙungiyar reshen Jami’ar Bayero, Comrade Lawan Musa Karaye, ya fitar a ranar Laraba, 06 ga watan Satumban da mu ke ciki, ya haƙurƙurtar da ɗaliban, ya na mai basu tabbacin cigaba da bibiyar lamarin daga ƙungiyar ta NAKSS, tare da yi musu albashirin cewar, Jami’ar ba zata rufe shafinta na rijista ba, har sai Gwamnatin Kano ta biya wa ɗaliban waɗancan kuɗaɗe.

“Bari nayi bayani da Hausa gwari-gwari domin kowa ya fahimci saƙon, kasancewar dukkanin yan asalin jihar Kano hausawa ne, kuma harshen Hausa shine yaren da kowa yake amfani dashi domin isar da saƙo, domin girmama takenmu na (Kano Jalla Babbar Hausa).

“Tun lokacin da gwamnatin jihar Kano ta fitar da sanarwar cewa, “zata biyawa ɗaliban jihar Kano dake karatu a jami’ar Bayero mutane 7000 kuɗin makaranta ne dai muke ta samun kiraye-kiraye da saƙonnin waya, kai wasu ma har gida suke zuwa domin jin ina aka kwana a matsayinmu na shuwagabannin ɗaliban jihar Kano dake BUK, duba da yanayi da aka shiga na an kulle ɗalibai a cikin duhu a sakamakon ƙarancin labarai da suke dasu akan wannan al’amari, haka ne yasa muke ta faɗi tashi da shige da fice don ganin cewa mun gamsar dasu tare da yayyafa ruwan sanyi a cikin zuciyoyinsu. A ƙoƙarin mu na haka mun bi matakai Da dama domin tabbatar da cewa munzo da bayanai sahihai.

“Shin wacce matsaya aka cimma tsakanin Gwamnatin jihar Kano da kuma jami’ar Bayero akan wannan al’amari?

“Tun kwanakin baya gwamnatin ta buƙaci jami’ar Bayero ta tura mata cikakken sunayen ɗaliban jihar Kano (adadin su) sannan ta ware mata sunayen ɗalibai da basu biya wannan kuɗin makaranta ba daban, sannan suma waɗanda suka biya a ware su daban. Tuni jami’ar Bayero ta aike da wannan sunayen.

“Shin wanne mataki gwamnatin jihar Kano ta ɗauka zuwa yanzu?

“Tun lokacin da gwamnatin jihar Kano ta karɓi wannan sunayen daga hannun jami’ar Bayero har yanzu bata fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da hanyar da zatabi don ganin ta biyawa ɗaliban jihar Kano wannan kuɗi ba, amma saidai mun san cewa ɗaya cikin abu guda 3 ne zai faru:

“1. imma dai gwamnati ta turo wa da jami’a kuɗin kai tsaye ta biya masu la’akari da cewa ɗaliban a hannunsu suke, kuma su kafi kowa sanin wadanda basu biya ba.

2. ko kuma kowanne ɗalibi ya cire REMITA ya aikewa da gwamnati ta biya masa da kanta.

3. ko kuma gwamnati ta tsara yadda zata bawa kowanne ɗalibi kuɗin sa yaje ya biya da kansa, kodai ta hanyar asusun banki ko kuma a basa kuɗin sa a hannu. Gwamnati ita tasan shirin da take da takamaimiyar hanyar da zata bi da kuma shirin da take gudanarwa.

“Shin wanne mataki BUK ta ɗauka dangane da wannan al’amari duba da cewar an kusa rufe biyan kuɗin makaranta?

“Babu shakka hankalin ɗalibai ya tashi matuƙa a sakamakon cewa an kusa rufe portal na makaranta kamar yadda aka ambata a baya, saidai a zaman meeting ɗin da mukayi da hukumar makaranta ta hannun Rijistara ta bamu tabbacin cewar zasu bar portal a buɗe har sai lokacin da gwamnatin Kano ta biyawa ɗalibai wannan kuɗi, ma’ana ba zasu rufe ba zai cigaba da zama a buɗe. Sun shaida mana cewa, kullum burinsu shine ɗalibai su samu su biya wannan kuɗin makaranta sannan yanzu ga dama ta samu to abun farin ciki ne a wajensu, kuma suma kansu jami’ar zata so a biya wannan kuɗi domin cigaba da tafiyar da wannan jami’ar yadda ya kamata.

“A taƙaice dai muna kira ga ɗaliban jihar Kano dake jami’ar Bayero da su kwantar da hankalinsu, jami’ar Bayero ba zata rufe biyan kuɗin makaranta ba, zata jira gwamnati har sai tazo ta biya wannan kuɗi.
Sannan muma jami’ar ta janyo mu a jika ta saka shugabancin ƙungiyar ɗaliban jihar Kano (NAKSS BUK CHAPTER) Aciki domin mu dinga samun cikakkun bayanai akan wannan al’amari.

“Shin Ko wanne mataki NAKSS BUK CHAPTER tayi bayan samun wannan cikakken bayani?

“Bayan samun waɗancan bayanai daga bakin hukumar makaranta wannan ƙungiyar bata tsaya nan ba tayi wani yunƙuri guda 4.

1. Wannan ƙungiya ta tuntuɓi kwamishinan ilimi mai zurfi domin jin ina aka kwana, sannan wanne shirye-shirye suke yi dangane da kuɗin makaranta da gwamnatin jihar Kano zata biyawa ɗalibai? suma a ɓangaren su suna ta shirye-shirye don ganin cewa anyi wannan abu cikin nasara.

2. Shugabancin wannan ƙungiya NAKSS munje Gidajen Radio domin tunatar da gwamnati da kira roƙo a gareka da tayi gaggawar juyowa kan wannan al’amari, munje Freedom Radio, munje Dala FM.

3. Mun buƙaci Hukumar makaranta ta bamu list na sunayen ɗaliban jihar Kano yan BUK, inda kai tsaye Rijistara ta turamu inda zamu je mu karɓa domin muma musan yadda abubuwa suke tafiya kada a barmu a duhu tunda mune zamu dinga samar da bayanai wa ɗalibai kai tsaye a koda yaushe.

4. Kai tsaye jami’a ta bamu dama da gudummawa sosai domin tabbatar da cewa muma shugabancin ɗalibai akwai rawar da zamu taka da ɓangaren hukumar makaranta da kuma ɓangaren gwamnati akan wannan al’amari. Don haka muna ta gudanar da ayyukanmu babu dare babu rana.

“Allah ya taimaki Jami’ar Bayero.
Allah ya taimaki jihar Kano.
Allah ya taimaki gwamnatin Kano.
Allah ya taimaki NAKSS BUK chapter.”

Sakataren kuɗin, ta bakin Kakaki, ya kuma ƙarƙare jawabin nasa da godiya ga Ɗaliban Jihar Kano, musamman waɗanda ke karatu a Jami’ar Bayero (BUK).

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button