Nishaɗi

Har Zaren Agogo Ya Tsinke, Ba Zan Bada Haƙuri Ga Ƴan Kannywood Ba – Abdallah Amdaz

Fitaccen Jarumi a Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Abdallah Amdaz, ya bayyana cewar, har zaren Agogo ya tsinke, ba kotu ba, babu wanda ya isa ya sanya shi, bayar da haƙuri ga Ƴan Masana’antar Kannywood.

Amdaz ya bayyana hakan ne, ta shafinsa na kafar sada zumunta da yammacin ranar Alhamis, inda ya yi wa rubutun ta ke da “Mun karɓa, kuma za mu bita da HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKIL”.

Kalaman nasa kuma, na a matsayin martani ne, kan ƙarar da Furodusa a masana’antar Kannywood, Alhaji Sheshe ya maka shi a gaban Kotu, ya na roƙon Kotun da ta tilasta wa Jarumin fitowa ya bayar da haƙuri cikin sa’o’i 48 ga ƴan masana’antar Kannywood, bisa zarginsa da furta kalaman ɓata suna ga ƴan masana’antar.

Sai dai, Amdaz ɗin ya ce, daga yanzu har Mahdy ya bayyana, a kuma busa ƙaho, bai ga Kotu ko Wani Ɗan Adam da ya isa ya sanya shi ƙaryata kansa ba. Ba kuma awanni 48 ba, har zaren Agogo ya tsinke babu wanda ya isa ya sanya shi bada haƙuri a cikin haƙƙin Ubangiji.

“Mun karɓi kuma zamu bita da HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKEEL.

“Amma ina son ku sani daga yanzu har Mahdy ya baiyana a busa ƙaho, banga kotu ko wani Ɗan Adam daya isa ya saka na ƙaryata kaina ba, ba awa 48 ba har zaren agogo ya tsinke, babu wanda ya isa ya sanyani bada haƙuri acikin haƙƙin Ubangijina ba.

“Duk abinda na faɗa na faɗa bazan ƙaryata kaina ba akan wannan maganar..”, a cewar Amdaz.

A ƙarshe, ya kuma shawarci ƴan masana’antar da su karɓi gaskiya su huta, su kuma yi umarni da kyakykyawa, su yi hani da mummuna, tun da sun kasa kawo hujja, ko ƙaryata abin da ya faɗa.

Ga abin da ya ke cewa, “Tunda kun kasa kawo hujja ko ƙaryata abinda na faɗa, kawai ku karɓi gaskiya ku huta, kuyi Umarni da kyakykyawa kuyi hani da mummuna.”

Abdallah Amdaz, ya fara fuskantar gagarumar suka, daga Manyan Jarumai, Masu Bada Umarni, Furodusoshi, da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood ne, tun bayan wasu kalamai da ya furta, a ya yin da ya halarci, kiran da hukumar Hisbah ta yi wa ƴan masana’antar a ranar Litinin, inda da dama daga cikinsu su ka cire shi daga Groups ɗinsu; ya yin da wasu kuwa su ke kiransa su na yi masa albishiri da cire shi daga cikin fina-finansu; har ma da masu barazanar maka shi a Kotu.

A cikin kalaman nasa a Hisbah, Amdaz ya ce, abu uku ne ya ke sanya jama’a shiga fim: Karuwanci; Kawalci; ko kuma dan neman ɗaukaka.

Ya kuma jaddada cewar, tabbas ɓarnar da ke cikin masana’antar ta Kannywood tana da yawa, dan haka akwai buƙatar gyara.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button