Harbe-Harben Bindigu Ya Kaure A Ya Yin Taron Ƙungiyar Ɗalibai Ta Ƙasa
Taron ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS), da ke cigaba da gudana, a International Conference Centre, da ke babban birnin tarayya Abuja, ya sauya salo zuwa harbe-harben bindigu.
Wurin taron dai ya hargitse ne, bayan fara jin harbe-harben bindigu a kusa da cibiyar da ake gudanar da taron.
Tuni dai, hankalin shuwagabannin Ɗaibai ya fara tashi, bayan fara aukuwar wannan lamari.
Wani faifan bidiyo, da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna yadda wakilan Ɗaliban su ke takewa da gudu, da nufin neman tsira, bayan da Jami’an ƴan sanda su ka fara harba barkonon tsohuwa, da nufin kwantar da tarzomar.
Tuni kuma aka garƙame manyan titunan da ke kaiwa ga Cibiyar ta International Conference Centre.
Ana zargin wani reshe na ƙungiyar ɗaliban ne da haddasa wannan lamari, bayan da su ka ƙuduri aniyar gudanar da zanga-zanga.