Labarai

Hatsarin Mota Na Kashe Mutane, Fiye Da Rashin Tsaro – Kakakin Ƴan sanda

Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewar Najeriya na fuskantar haɗurran ababen hawa akan tituna, fiye da sauran ƙasashe.

Adejobi, ya ce haɗurran motocin na kashe jama’ar ƙasa, fiye da yadda matsalolin rashin tsaro ke murƙushe rayuka, la’akari da bayanan da ke tattare a ofisoshin ƴan sanda.

Kakakin ƴan sandan, ya bayyana hakan ne, ranar Laraba, ta shafinsa na kafar sada zumunta ta X, ya yin da ya ke martani ga wani mutum, da ya buƙaci Sufeto Janar na rundunar ƴan sanda, IGP Kayode Egbetokun, da ya halarci Taron Jami’an Ƴan Sanda na duniya, a Dubai, da ke haɗaɗɗiyar Daukar Larabawa, da ya nazarci yadda Jami’an ƴan sanda ke gudanar da aikin rage afkuwar haɗurran motoci, a ƙasar.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button