Hauhawar Farashi Zai Jefa Ƴan Najeriya Miliyan 2.8 Cikin Fatara – Cewar Bankin Duniya
Hauhawar farashi, da ma rashin rashin haɓɓakar tattalin arziƙin ƙasa, zai jefa al’ummar Najeriya sama da miliyan 2.8 cikin tsantsar fatara, zuwa ƙarshen wannan shekarar da mu ke ciki (2023).
Bayanin hakan, na ɗauke ne ta cikin wani rahoto da bankin duniya ya fitar, mai taken, “Ƙididdiga ƙasa da ƙasa, kan cigaban duniya’.
Bankin, wanda ke da matsugunni a birnin Washington, ya ce, “Zuwa ƙarshen shekarar 2023, tashin farashin kayayyaki, da rashin cigaban tattalin arziƙi zai taka gagarumar rawa waje jefa ƴan Najeriya kimanin miliyan 2.8 cikin talauci, wanda hakan ke wakiltar kaso 0.4 na yawan al’ummar ƙasar, hakan kuma zai ƙara yawan mutanen da ke cikin fatara, zuwa sama da kaso 37.5”.
Bankin ya kuma yi hasashen fara raguwar yawan matalautan, zuwa farkon shekarar 2024.