Hisbah Ta Gayyaci Mata Ƴan TikTok Da Ƴan Facebook
Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta gayyaci ɗaukacin Matan da ke amfani da kafafen sada zumunta na TikTok da Facebook, zuwa babbar helikwatarta, da ke Sharaɗa, a ranar Litinin, 06 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, da misalin ƙarfe 4 na yammaci, domin ganawa da Babban Kwamandan Hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar, Dr. Mujahid Aminuddeen, shi ne ya sanar da saƙon gayyatar, da yammacin ranar Juma’a.
Inda ya ce, hukumar na buƙatar ganawa da Matan da ke amfani da kafafen sada zumuntar da ma ƴan kwalta ne, domin lalubo musu mafita, tare da samar musu sana’o’in dogaro da kai, da nufin sauya su daga yadda su ke gudanar da fitsara da rashin kunya a shafukan, da ma kan tituna, zuwa mutane na ƙwarai da al’umma za ta amfana.
Aminuddeen, ya kuma buƙaci matan da za su halarci taron ganawar da su halarci ofishin cikin shiga ta mutunci, sanye da hijabi da niƙabi, domin kare martaba da kimar kansu.
Ka zalika, ya buƙaci dukkannin waɗanda su ka yi karatu daga cikinsu, da su je tare da takardun karatunsu, ya yin da su ma masu ƙwarewa a fagen sana’a ake buƙatar su je da nasu takardun sana’ar.