Hisbah Ta Hana Masu Sana’ar DJ Zuwa Bikin Mata, A Kano
Hukumar HISBAH ta jihar Kano, ta hana Maza masu gudanar da sana’ar kaɗe-kaɗe (DJ) a jihar, halartar dukkannin wani biki na mata.
Babban Kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron tattaunawa da hukumar ta gudanar da masu sana’ar ta DJ, ya ce ɗaukar matakin ya zama wajibi domin kare cakuɗuwar da Maza da Mata ke yi, a yayin bukukuwa.
Daurawa ya ce, daga wannan lokaci, Mata ne kaɗai za su dinga halartar bukukuwan Mata.
Ya na mai cewar, “A matsayin Kano na jihar Musulunci, ba za mu lamunci cakuɗuwar Maza da Mata a biki guda ba. Saboda hakan abu ne na rashin tarbiyya”.
Daurawa, ya kuma ce sun gudanar da wani zaman tattaunawar da masu Event Centres, dukka da nufin lalubo hanyoyin tsaftace tsare-tsarensu, tare da tabbatar da sun yi biyayya ga dokokin gudanar da ayyukansu.
A nasa jawabin, wakilin masu gudanar da Sana’ar DJ, Ibrahim Abdullahi, wanda shi ma mai gudanar da sana’ar ne a unguwar Farawa, ya yabawa hukumar bisa gayyatarsu da ta yi, ta kuma nusar da su kan tsare-tsarenta akan ayyukansu.
Ibrahim, ya ce wajibi ne ga dukkannin masu sana’ar DJ a jihar, su yi biyayya ga wannan umarni, ko kuma su fuskanci hukunci.