Zamantakewa

HISBAH TA KAMA MATUƘAN ADAI-DAITA SAHU 52, SABODA ASKIN BANZA

Hukumar HISBAH ta jihar Kano, ta kama matuƙa baburan Adai-daita sahu guda 52 a jihar, saboda samunsu da yin “askin rashin tarbiyya”, sayar da miyagun ƙwayoyi, da kuma cuɗanya Maza da Mata a cikin baburansu.

An kuma kama Matasan ne a sassa daban-daban na ƙwaryar birnin Kano.

A baya-bayan nan ne dai, hukumar ta HISBAH ta ƙaddamar da wani gangami mai taken, “Operation Kau Da Badala”, a wani yunƙuri na kakkaɓe ayyukan rashin tarbiyya, kamar yawon ta zubar, caca, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, saye da sayarwar barasa, da makamantansu, a tsakanin matasan jihar.

Mataimakin babban Kwamandan rundunar na Kano, Mujahid Aminuddeen, wanda ya gabatar da jawabi ga Matasan kimanin 52 da HISBAH ta cafke, a ranar Juma’a, ya roƙe su da su kasance Jakadu na gari ga Musulunci, jihar Kano, da ma al’ummar da su ke zaune a cikinta.

Ya kuma ce, hukumar za ta cigaba da gudanar da aikin zaƙulo ire-iren matasan da ke aikata wannan rashin ta Ido, dan tabbatar da an kawo ƙarshen aikata munanan aikace-aikacen da ke da nasaba da rashin tarbiyya, a faɗin jihar.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button