HISBAH Ta Yi Martani Kan Batun Garƙame Asusan Ajiyarta Na Banki
Hukumar HISBAH ta jihar Kano, ta bayyana cewar, an garƙame dukkannin asusan ajiyarta, bayan da mamallaka wuraren saukar baƙi (Hotels), su ka maka ta ƙara a gaban Kotu.
Babban Kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shi ne ya tabbatar da hakan, ranar Laraba, ya yin zantawarsa da TRT Hausa.
Idan za a iya tunawa dai, a watannin da su ka gabata, hukumar ta HISBAH ta kai sumame wasu daga cikin Hotel-Hotel ɗin jihar, tare da wuraren nishaɗi mabanbanta, bisa zargin sheƙe aya, da aikata rashin ta ido, a wuraren.
Daurawa ya ce, “Eh, da gaske ne an rufe dukkannin asusan bankunanmu. Na kuma tura wakili dan tattaunawa da Atoni Janar kan batun.
“Mun karɓi takardar Kotu, da ke bayyana zarginmu da wasu Hotel biyu su ke yi, wanda ya sanya aka caje mu Naira 700,000 da 100,000. Inda takardar ta buƙaci mu biya jimillar Naira 800,000, hakan ne ma ya sa aka rufe asusan ajiyartamu.
“Muna son a sanar damu laifin da mu ka aikata, domin sanya Lauyoyinmu su bibiya. Idan mu ka gaza kare kanmu, to sai a yi mana hukunci.”
Daurawan, ya kuma bayyana damuwa kan yadda rufe asusan, ke cigaba da haifar da tasgaro, a cikin ayyukan hukumar.