Nishaɗi

HISBAH Za Ta Sake Gayyatar Ƴan Kannywood A Karo Na Biyu, Bayan Bijirewa Kiran Farko

Hukumar HISBAH ta jihar Kano, ta bayyana cewar, za ta sake gayyatar ƴan masana’antar Kannywood a karo na biyu, ta irin hanyar da su ke buƙata, domin tattaunawa da su, da kuma yi musu nasiha, bayan da su ka bijirewa amsa kiran hukumar a karon farko.

Shugaban hukumar ta Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shi ne ya bayyana hakan, ya yin da ya karɓi baƙuncin shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano.

Idan ba a manta ba dai, a makon da ya gabata ne, hukumar ta Hisbah ta fitar da sanarwar gayyatar ɗaukacin Masu Bada Umarni, Masu Ɗaukar Nauyi, Marubuta, da ma Jaruman Masana’antar ta Kannywood zuwa Helikwatarta ta jiha, da ke Sharaɗa Phase III, sai dai ɗai-ɗaiku daga cikinsu ne su ka samu halarta, bayan da da dama daga ciki su ka ƙi zuwa, bisa hujjar rashin gayyatarsu ta hanyar da ta dace, wato ta hanyar ƙungiyoyinsu.

Da ya ke bayyana matsayin hukumar ta HISBAH kan lamarin, Daurawa ya ce, a wannan karon hukumar za ta gayyace su ta hanyar da su ke buƙata, domin ko a baya rashin sanin ƙungiyoyin nasu ne ya sanya hukumar ta gayyace su ta hannun hukumar tace fina-finai, da kafafen yaɗa labarai.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button