Wasanni
Hotuna: Yadda Ronaldo Ya Yi Shigar Larabawa
Wasu hotuna da shafin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Nassr ya wallafa, ya nuna yadda fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan na duniya, wanda ke taka leda a ƙungiyar ya caɓa ado cikin shigar Larabawa, tare da riƙe takobi.
A gefe guda kuma, an hangi ɗan wasa, Sadio Mane shi ma, cikin irin wannan shiga.
Rahotanni, sun bayyana cewar, an ɗauki hotunan ne, a ya yin bikin cikar ƙasar Saudi Arabia shekaru 93 da kafuwa.
A baya-bayan nan dai, rahotanni sun ta alamta yiwuwar Musuluntar ɗan wasa, Christiano Ronaldo, sakamakon yadda ya ke yawan kutsa kansa cikin al’amuran da su ka shafi Addinin Musulunci, da dama.
Amma Ya Ku Ka Kalli Wankan Nasa ?
Ku bayyana mana amsoshinku a sashen bayyana ra’ayi (Comment Section).