Labarai

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano, Ta Tseratar Da Rayuka 25, A Watan Janairu

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta bayyana yadda ta samu nasarar tseratar da rayuka 25, tare da dukiyoyi na sama da Naira miliyan 95, a cikin gobara 70 da ta tashi, a watan Janairun da ya gabata.

Bayanin hakan na ɗauke ne, ta cikin wani jawabi da Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, ya fitar, a ranar Talata.

Abdullahi, ya kuma ce, mutane biyu sun rasa rayukansu, ya yin da aka rasa dukiyar Naira miliyan 40, a tashe-tashen gobarar.

“Mun amsa kiraye-kirayen neman agaji guda tara, mun kuma samu kiran ƙarya guda 11”, a cewarsa.

Inda a ƙarshe ya ƙara da shawatar jama’ar jihar, da su kasance masu kaffa-kaffa a ya yin da su ke amfani da wuta, musammanma a wannan yanayi da ake ciki na sanyi.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button