Zamantakewa

Hukumar Kashe Gobara Ta Tseratar Da Rayuka 64 A Jihar Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta ce Jamiánta sun samu nasarar tseratar da rayukan kimanin mutane 64, a lokutan gobara mabanbanta cikin watan Afrilun da ya gabata.

Ya yin da mutane 23 su ka rasa rayukansu daga kamawar wutar, dukka dai a watan na Afrilu. Wani jawabi da Kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ya fitar, a ranar Talata, ya ce Jamián nasu sun kuma samu nasarar tseratar da kadarorin da kimarsu ta kai Naira miliyan 73, da dubu 195, sai kuma kadarorin sama da miliyan 29, da dubu 90 da gobarar ta cinye kurmus. A kuma watan na Afrilu dai, hukumar ta samu kiraye-kirayen neman agaji a Ofisoshinta guda 27 da ke fadin jihar nan, inda kirayen tashin gobara su ka kai kimanin 83, sai wasu kiraye-kirayen neman agajin da ba gobara ba kimanin 45, ya yin da kiraye-kiraye 12 su ka kasance na karya.

Jawabin ya kuma bukaci mazauna jihar nan da su sake sanya lura ta musamman, tare da kare kawunansu, ta hanyar daina hura wutar da ba a bukata.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button