Hukumar Kula Da Shige Da Fice Ta Samar Da Fasfo 60,000 A Kwanaki 4
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya tabbatar da cewar, sun yi nasarar samar da Fasfo kimanin 60,000 da ya yi wa hukumar kwantai cikin kwanaki huɗu kacal, inda a yanzu su ke da buƙatun samar da Fasfo 200,000.
An cimma wannan nasara ne kuma, bayan umarnin da Ministan ya bawa hukumar lura da shige da fice ta Immigration, na tabbatar da ta sallami dukkannin kwantan Fasfo ɗin da ake binta, cikin makonni biyu.
Tunji-Ojo, ya kuma bayyana hakan ne, ya yin da Ministar Al’amuran jinƙai da fatattakar fatara, Dr. Betta Edu, ta kai masa ziyara, ranar Talata, a babban birnin tarayya Abuja.
A cewar rahoton da Mai Bawa Ministan Shawara kan yaɗa Labarai, Alao Babatunde ya fitar dai, An jiyo Tunji-Ojo ɗin na bayyana cewar, zai kawo ƙarshen wahalhalun da ake fuskanta wajen mallakar fasfo a ƙasar nan.
“Ya yin da mu ka shiga Ofishi, mun samu cewar, matsalolin cunkushewar Fasfo sun yi yawa, kuma mun sha alwashin cewar, ba zamu bari matsalar ta cigaba ba.
“Zuwa safiyar nan, zan iya bayyana muku cewar, mun samar da Fasfo sama da 60,000 da ake binmu.
“Ya yin da na zo Ofis a ranar 6 ga watan Satumba, na bada wa’adin makonni biyu, wajen ganin an biya bashin Fasfo sama da 200,000 da Jama’a su ke binmu. Har yanzu kuma Ina cigaba da maimaita matsayata ta cewar, wajibi ne mu kawo ƙarshen wannan matsalar”, a cewarsa.
A nata jawabin tun da fari, Ministar ta harkokin jin ƙai, ta bayyana cewar maƙasudin kai ziyarar tasu shi ne buƙatar Ma’aikatun biyu su haɗa kai, wajen rage yawaitar safarar bil-Adama.
Ta kuma ce, haɗin kan zai taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan matsalar rashin Aikin yi, da ma rage fatara, a tsakanin al’umma.