Tsaigumi

Hukumar Kula Da Zirga-Zirga Ta Yi Awon Gaba Da Motar Sojoji, Bisa Zargin Ajiyeta A Inda Bai Dace Ba

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Lagos, ta ɗauke wata Motar Sojoji, bayan samun Jami’an Sojin barikin yankin Mile 2, da ke jihar Lagos, da ajiyeta ba a inda ya dace ba.

Bayanin hakan, na ɗauke ne ta cikin wani saƙo da hukumar ta LASTMA ta wallafa a shafinta na kafar sada zumunta ta X, a yau (Lahadi).

An kuma wallafa saƙon ne ɗauke da hotuna, inda hukumar ke cewa, “Biyo bayan samun ƙorafin masu ababen hawa, game da wata babbar Motar Sojoji da aka ajiye a tsakiyar titin da ke gaban barikin Soji ta yankin Mile 2, da ke dab da gadar zuwa Orile.

“Daraktan Ayyuka na LASTMA, Peter Gbejemede, ya jagoranci tawagar Jami’an wannan hukuma zuwa wurin, tare da ɗauke motar daga tsakiyar titi”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button