Kotu
Hukuncin Farko: Abba Sahihin Ɗan Jam’iyyar NNPP Ne – Kotun Zaɓe
Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan jihar Kano, ta tabbatar da cewar, Gwamna Abba Kabir Yusuf halastaccen ɗan jam’iyyar NNPP ne, saɓanin iƙirarin da jam’iyyar APC ta yi, na cewar zaɓaɓɓen Gwamnan ba halastaccen ɗan APC bane.
Kotun ta kuma bayyana cewar, sha’anin kasancewar ɗan takara halastaccen ɗan jam’iyya ko akasin haka, hurumin cikin gida ne, na jam’iyyar da ya ke ciki, dan haka jam’iyyar APC bata da hurumin ƙalubalantarsa akan wannan.
Jam’iyyar APC dai, ta buƙaci Kotun sauraron ƙarar zaɓen da ta soke nasarar da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya samu, bisa zargin rashin kasancewarsa sahihin ɗan jam’iyyar da ya yi takara a cikinta ta NNPP.