Ilimi Zai Magance Kowacce Irin Matsala A Masana’antar Kannywood – Abubakar Sani
Fitaccen Mawaƙi, wanda ya ga jiya, ya ga yau a Masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), Abubakar Sani, ya bayyana cewar Ilimi zai shawo kan kowacce matsala da Masana’antar ke fuskanta.
Abubakar Sani, ya bayyana hakan ne, ya yin da ya ke zantawa da tashar Freedom Radio Kano, a ranar Alhamis, kan batun sabunta rijistar ƴan masana’antar Kannywood, da hukumar tace fina-finai ta bijiro da shi.
Abubakar Sani yace, a halin yanzu, Ilimi ƴan masana’antar su ka fi buƙata, ba sauya rijista ba, kuma da za a samar musu da Ilimi, babu shakka da kansu za su je su yi rijistar, ko da ba sai an kai ruwa rana ba.
Mawaƙin dai, ya buƙaci hukumar ta tace fina-finai da ta haɗa kai da Gwamnatin Kano, wajen mayar da membobin masana’antar Makaranta, bayan kammala gyare-gyare a Film Academy, da tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya samar.
Ka zalika ya ƙara da miƙa buƙatar ganin an raba kuɗaɗen makarantar kashi biyu, Gwamnati ta biyawa ƴan Kannywood ɗin rabi, su ma su biya rabi, kamar yadda ta yi a sauran manyan Makarantu.
Sani, ya kuma ce, ƙaramar kasuwar faifan Sidi ta Film ta mutu, a yanzu babu hanyar da Ƴan Kannywood ke sayar da fina-finansu idan ba ta tashoshin Talabijin, da YouTube ba, bayan kuma akwai ɗumbin hanyoyin sayar da Film da za a iya ganowa idan aka samu Ilimi.
Bugu da ƙari Sani, ya bayyana buƙatar ganin Hukumar ta tace fina-finai ta tsaya kai da fata wajen kare haƙƙoƙin mallakar ƴan masana’antar ta, duba da yadda wasu kafafen Talabijin da na Rediyo su ke sanya Fina-Finai da waƙoƙinsu ba tare da biyan lada ba.