Kasuwanci

Illar Da Rufe Iyakar Nijar Ke Wa Tattalin Arziƙin Najeriya – Sanata Aliero

Ɗan Majalissar Dattijai mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Sanata Adamu Aliero, ya bayyana cewar, rufe Iyakar Najeriya da Nijar da Gwamnatin tarayya ta yi, abu ne da ke da matuƙar illa ga tattalin arziƙin ƙasa nan, musammanma jihohin da ke kusa da iyakar.

Aliero, wanda ya kasance tsohon Gwamnan jihar Kebbi (zango biyu), ya bayyana hakan ne, ya yin da ya ke zantawa da tashar Arise, a yau (Talata), ya na mai cewar ɗaukar matakin rufe iyaka tsakanin ƙasashen guda biyu, waɗanda dukkanninsu su ke cikin ECOWAS ba dai-dai bane, kuma mataki ne da ya kamata a yi mi’ara koma baya game da shi.

Ya kuma ce, Ƴan Majalissun tarayyar da su ka fito daga yankunan jihohin da lamarin ya fi shafa, a Arewacin Najeriya sun zauna sun tattauna, tare da kira ga Gwamnatin tarayya, da ta ɗauki matakin gaggawa kan lamarin, ta hanyar sake buɗe iyakar, don ganin an cigaba da gudanar da al’amuran koyo da koyarwa.

“Idan ka je kan iyakar a yau, za ka ga yadda dubban motocin dakon kaya su ke dawowa cikin ƙasar nan, ɗauke da kaya niƙi-niƙi daga ƙasashen ƙetare, amma an tsare su akan boda, saboda takunkumin ECOWAS.

“Hatta yarjejeniyarmu ta fannin wutar lantarki ma an karyata, bayan da gwamnati ta katse wutar da ta ke bawa ƙasar ta Jamhuriyyar Nijar “, a cewar Aliero.

Aliero, wanda kuma tsohon Minista ne, ya ce ƙasashe da dama, basa amfani da takunkumin da ECOWAS ɗin ta ƙaƙabawa Jamhuriyyar Nijar, amma Najeriya ta ɗauka ta yafa.

Idan za a iya tunawa dai, ECOWAS ta ƙaƙabawa Jamhuriyyar Nijar ɗin takunkumi ne, sakamakon juyin mulkin soji da ta fuskanta, inda ta turje kan cewar ba za ta cire takunkumin ba, har sai ƙasar ta sake rungumar tsarin Demokraɗiyya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button