Siyasa

Ina Da Yaƙinin APC Za Ta Sake Lashe Zaɓen Shugabancin Ƙasa, A Shekarar 2027 – Mataimakin Shugaban Majalissar Wakilai

Mataimakin shugaban Majalissar Wakilai ta tarayya, Benjamin Kalu, ya bayyana ƙwarin guiwar da ya ke da shi, kan cewar, Jam’iyyarsa ta APC, za ta sake lashe zaɓen shugabancin ƙasa, na shekarar 2027.

Kalu, wanda ya bayyana hakan, a ya yin taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar a jihar Abia, da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja, ya ce da dama daga cikin al’ummar Najeriya, su na kan hanyar tsunduma cikin jam’iyyar mai mulki ta APC.

A gefe guda kuma, ya nemi afuwa, tare da haƙurƙurtar da fusatattun membobin jam’iyyar, ya na mai cewar, hakan ne kawai matsalarsu gabanin lashe zaɓukan gaba.

Ya na mai cewar, “Ina mai tabbatar muku, APC za ta sake lashe zaɓen 2027. Tun yanzu ya kamata mu fara ƙoƙarin sanya jam’iyyarmu a gaba. Duk wanda aka ɓatawa, muna neman afuwarsa, muna buƙatar haɗa hannu, dan ciyar da jam’iyyarmu gaba.”

Kalu, ya kuma buƙaci mayar da dukkannin membobin jam’iyyar da aka dakatar, a jihar ta Abia, ya na mai jaddada cewar, hakan ne kawai zai tabbatar da ɗorewar zaman lafiya, da haɗin kai.

A nasa jawabin tun da fari, shugaban zauren masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC na jihar Abia, Chris Adighije, ya ce zaman lafiya da haɗin kai shi ne babban abin da mataimakin Majalissar ta wakilai ya ke fatan gani a APCn jihar.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button