Ina Dukan Matata Ne, Domin Nuna Mata Hanya – A Cewar Wani Magidanci Ya Yin Da Ya Bayyana A Kotu
Wani Magidanci mai yara huɗu, Lukman Soladoye, ya bayyana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci, da ke Magajin Gari, a jihar Kaduna, bisa zarginsa da laifin lakaɗawa Matarsa, Kemi Soladoye, tare da yaransu guda huɗu duka.
Soladoye, ya bayyanawa Kotun cewar, ya na dukan Matarsa da Yaran nasa ne idan su ka yi kuskure, ya na mai ƙarawa da bayyana yadda ya ke matuƙar ƙaunar Iyalan nasa, tare da yi musu fatan wanyewa lafiya.
Tun da farko, Mai ƙara ce dai, ta hannun Lauyanta, B.A Tanko ta buƙaci Kotun da ta sanya Mijin nata ya sake ta, sakamakon yawan dukanta da ya ke yi, wanda hakan ne ya sanya ta sauya ra’ayinta a zama da shi.
Ta kuma roƙi Kotun, da ta tilasta wanda ake ƙara (Mijinta), da ya daina cin zalinta, tare da ƴaƴayen nasu.
Alƙalin Kotun, Isiyaku Abdulrahman, ya tambayi wanda ake ƙara ko zai iya daina dukan Matarsa, da ƴaƴan nasa ?, Inda ya amsa da Eh, zai daina dukan Matar, amma banda yaransa a cikin wannan alƙawari.
Sai dai, Alƙalin Kotun ya bashi shawarar cewa, “A matsayinsu na yaranka, duka ba shi ne hanyar da zai gyara su ba; ko da yaushe ka dinga nuna musu ƙauna da jawo su a jiki; ka yi musu Addu’a, ka kuma basu shawarwari”.
Alƙalin, ya ce Kotun za ta cigaba da sanya ldanu akan ɗabi’un wanda ake ƙarar, inda ya buƙaci Matar da ta sanar da Kotun, muddin Mijin nata ya sake dukanta, ko wai nau’i na cin zarafi.