INEC Ta Fara Tantance Jam’iyyun Siyasa
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta fara gudanar da aikin tantance jam’iyyun siyasar ƙasar nan, kamar yadda kundin dokokin ƙasa ya kallafa mata.
Daraktar al’amuran zaɓe da sanya Ido kan jam’iyyun Siyasa, Hawa Habibu, ita ce ta bayyana hakan, ya yin da ta jagoranci tawagar sanya Ido a zaɓuka da jam’iyyun siyasa na hukumar ta INEC, zuwa ziyarar da su kaiwa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Inda Hawa ɗin ta ce, ziyarar tasu, wani ɓangare ne na aikin tantance jam’iyyu da hukumar ke gudanarwa.
“Alhaki ne da kundin tsarin dokokin ƙasa ya kallafa mana, mu bincika, tare da zaƙulo jam’iyyun da basa biyayya ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ƙasa.
“Muna tantance yadda tsarin jam’iyyun ya ke, da irin kuɗaɗen da su ke kashewa, da makamantansu”, a cewarta.
A nasa jawabin, Abdullahi Umar Ganduje, ya yabawa ƙoƙarin hukumar ta INEC bisa wannan gagarumin aiki da ta ke gudanarwa, da ma tsaiwar gwamen jakin da ta yi, wajen tabbatar da inganta tsarin zaɓukan ƙasar nan, duk kuwa da tarin ƙalubalen da ake fuskanta.
Ganduje, ya kuma ce abubuwa marasa daɗin da su ke faruwa kafin, da bayan zaɓe abubuwa ne da ƴan siyasa ke hura wutar ruruwarsu.
Ya kuma bayyana ziyarar a matsayin abar tarihi, kuma wata dama da INEC da jam’iyyun siyasa za su ƙara kyautata alaƙarsu da ita, musamman ma jam’iyyar APC.
Ka zalika, ya ce tuni jam’iyyar ta miƙa dukkannin bayanan da hukumar ta ke buƙata.