Kasuwanci

Instagram Zai Fara Biyan Ƴan Najeriya

Shahararren dandalin nan na sada zumunta, da ya yi shura a faɗin duniya, ta fuskar wallafa hotuna da gajerun bidiyoyi, Instagram, ya bayyana shirinsa na fara biyan ƴan Najeriyar da ke wallafa bayanai a cikinsa, a nan gaba kaɗan.

Shugaban kula da al’amuran ƙasashen duniya na kamfanin Meta, Sir Nick Clegg, shi ne ya bayyana hakan, ya yin da ya jagoranci tawagar kamfanin na Meta, zuwa fadar mulki ta Villa, domin kai ziyara ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis.

Clegg, ya ce kamfanin na da tarin shirye-shirye ga ƴan Najeriya, kuma ya shirya haɗa kai da ƙasar.

Clegg, ya kuma godewa shugaban ƙasar, bisa damar da ya bayar ta sanya igiyar sadarwar kamfanin a ƙarƙashin tekun Najeriya

Da ya juya kan batun fara biyan ƴan Najeriyar, Clegg wanda tsohon Mataimakin Fira-Ministan Burtaniya ne ya ce, za a ƙaddamar da tsarin ne a watan Yuni.

A nasa ɓangaren, Ministan sadarwa na Najeriya, Dr. Bosun Tijani, ya ce Kamfanin Meta muhimmin sha’ani ne a Najeriya, kuma ana maraba da buƙatar kamfanin na haɗa kai da gwamnati, wajen bunƙasa fannin tattalin arziƙin ƙasa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button