Nishaɗi
Iyaye Sun Hana Saurayi Auren Ƴarsu, Bayan Samun Spill Over A Jami’a
Wasu Iyaye sun fasa Aurar da Ƴarsu ga Saurayin da aka yi musu baiko, bayan da su ka gano cewar, saurayin ya na da Spill Over, a Jami’ar da ya ke karatu.
Iyayen budurwar dai sun ce wajibi ne su ɗauki wannan mataki, domin ƙauracewa fargabar da su ke na samun Jikokin da su ma za su gaji wannan Spill Over.
Iyayen sun kuma gano wannan gagarumar ɓaraka ne, ya yin da ya rage mako guda ɗiyar tasu ta Angwance da Masoyin nata.
Wannan sha’ani kuma shi ake cewa, ” Allah Ɗaya – Gari Bambam”.
To ko nan gaba sai mai “First Class” za a dinga bawa Aure🤔, “Oho!”.