Jagoran Masu Horas Da Ƴan Wasan Super Eagles Ya Bayyana Ƙwarin Guiwa Kan Victor Osimhen
Jagoran masu horas da ƴan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasa, Super Eagles, Jose Paseiro ya bayyana irin ƙwarin gwuiwar da ya ke da shi, akan ɗan wasan baya na tawagar, Victor Osimhen, na cigaba da taka gagarumar rawa wajen ɗaukaka sunan tawagar, bayan dawowarsa daga jiyyar raunin da ya samu, a ya yin wani wasan ƙasa da ƙasa da Najeriya ta fafata.
Dan wasan, wanda ke taka rawa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli, ya samu raunin ne a wasan da tawagar Najeriya ta tashi kunnen doki 2-2 da ƙasar Saudi Arabia, a watan Oktoban da ya gabata, kuma bai ƙara taka leda a ƙungiyar Napoli ba, tun bayan ƙwallon da ya zura a wasansu da Fiorentina, tun a ranar 8 ga watan Oktoba.
Ɗan wasan ya zauna a Najeriya sama da tsawon mako guda, kafin komawarsa zuwa gasar Italiya, a yau Laraba, amma ba zai kasance a gasar UEFA League wacce za su kece raini da Union Berlin ba.
Idan ba a mantaba dai, a makon da ya gabata ne, aka bayyana ɗan wasa Osimhen a matsayin wanda ya ƙare a matsayi na takwas a Ballon dÓr ta wannan shekarar, wacce Lionel Messi ya lashe, inda aka kuma ayyana shi a matsayin gwarzon ɗan wasan CAF na shekarar 2023, wanda ake shirin miƙa masa kyautar karramawar a ranar 11 ga watan Disamban wannan shekarar.