JAMB Ta Saki Sakamakon Ɗalibai 36,540 Daga Cikin 64,000 Da Ta Riƙe Sakamakonsu
Hukumar shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantu ta ƙasa, JAMB, ta saki ƙarin sakamakon jarrabawar UTME ta ɗalibai 36,540 da ta riƙe a baya.
Bayan sakin waɗannan ƙarin sakamakon kuma, a yanzu hukumar ta saki jimillar sakamakon ɗalibai 1,879,437, a cewar wani jawabi da mai magana da yawun hukumar ta JAMB, Fabian Benjamin ya fitar.
Hukumar, ta kuma ce har yanzu akwai sakamakon ɗalibai 26,000 da su ke cigaba da zama a hannunta, yayin da take cigaba da gudanar da bincike akai, bisa zarge-zargen satar jarrabawa.
JAMB ta kuma buƙaci ɗaliban da aka riƙe sakamakon jarrabawarsu a baya, da su sake duba sakamakon, dan tantance ko ya na daga cikin waɗanda aka saki.
Ɗalibai, za su iya duba sakamakon ne, ta hanyar aikewa da saƙon UTMERESULT zuwa lambar 55019, akan kuɗi Naira 50.