Ilimi

JAMB Ta Sanya Ranar Da Zata Sake Rubuta wa Ɗalibai Jarrabawa

Hukumar shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB), ta bayyana cewar, za ta gudanar da jarrabawa a ranar 6 ga watan Mayu, ga dukkannin ɗaliban da basu samu damar rubuta jarrabawar ba, sakamakon wasu matsaloli da su ka fuskanta.

Bayanin hakan, na ɗauke ne, ta cikin wani jawabi da kakakin hukumar, Dr. Fabian Benjamin ya fitar, ranar Litinin, a babban birnin tarayya Abuja.

Benjamin ya ce, dukkannin ɗaliban da ke cikin rukunonin da aka tantance a cibiyoyin rubuta jarrabawa, sai dai basu samu damar rubutawa ba, sakamakon matsalolin dangwalen ƴan yatsu, da ma rashin dai-daitar bayanansu, su ne za su amfana da wannan dama.

Daga cikin ɗalibai 1,586,765 da su ka nuna sha’awarsu ta rubuta jarrabawar ta UTME a wannan shekarar dai, 80,166 ne wannan matsalar ta shafa.

Benjamin, ya kuma ce, hukumar ta amince da sanya ranar Asabar, 6 ga watan Mayun, domin sake gudanarwa da ire-iren waɗannan ɗalibai jarrabawar ne, bayan taron gaggawar da ta gudanar, da masu ruwa da tsakinta, a ranar 30 ga watan Afrilun da ya gabata.

Ka zalika Benjamin, ya ce za a saki sakamakon ɗaliban da su ka riga su ka rubuta jarrabawar a ranar 2 ga watan Mayu.

Ya kuma ce, hukumar taƙi sakin sakamakon jarrabawoyin ɗaliban da wuri ne, domin kammala tantancewa da ma tabbatar da sahihancinsa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button