Ilimi

JAMB Ta Wajabta Zuwa CBT Centres Da Wayoyi, Ga Ɗaliban Da Za Su Yi Rijista

√• JAMB Ta Wajabta Zuwa CBT Centres Da Wayoyi, Ga Ɗaliban Da Za Su Yi Rijista

√• Sama Da Ɗalibai 600,000 Ne Su Ka Yi Rijistar JAMB, Cikin Makonni Biyu

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••

A wani mataki na ƙara tsaftace tsare-tsaren rijistar jarrabawar JAMB UTME ta shekarar 2024, da ke cigaba da gudana, hukumar JAMB ta bayyana cewa, daga yanzu wajibi ne duk ɗalibin da zai yi rijista, ya halarci CBT Centre tare da wayarsa ta hannu.

Hakan kuma na nufin, daga wannan lokaci, hukumar bata amince Ɗalibi ya je da Profile Codes ɗin da aka turo masa, bayan aika saƙon NIN zuwa 55019 ko 66019 a takarda ba, haka zalika waɗanda ke sayen ePIN daga gida kafin halartar CBT Centres ma, daga wannan lokaci wajibi ne su nuna saƙon PIN ɗin da aka tura musu a Message, kafin samun damar yin rijista.

++++++++++++++++++++++++

A fannin ƙididdigar adadin Ɗaliban da su ka yi rijistar jarrabawar, daga fara rijista zuwa yanzu kuwa, JAMB ta ce sama da Ɗalibai 695,361 ne su ka yi rijista.

Ya yin da a gefe guda, hukumar ta biya CBT Centres kuɗin rijistar Ɗalibai 422,434, da su ka yi rijista zuwa ranar Juma’a.

DOMIN TAMBAYA, KO NEMAN SHIGA ASOF JAMB GROUP, KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR : 08039411956.

Rubutawa : Miftahu Ahmad Panda.

08039411956

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button