Ilimi

JAMB ta yi Allah-Wadai Da Matakin Jami’ar Bauchi, Na Riƙe Sakamakon Ɗalibai

Hukumar shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB), ta bayyana rashin jindaɗinta, kan matakin da Jami’ar Jihar Bauchi, da ke Gadau ta ɗauka, na riƙe sakamakon jarrabawar Ɗaliban da su ka kammala makarantar a wannan shekarar, sakamakon gagarumin bikin nuna farincikin kammala makarantar, da su ka gudanar.

JAMB ta bayyana rashin jindaɗinta game da matakin ne, ta cikin jadawalinta na mako-mako, da ta fitar a ranar Litinin.

Idan ba a manta ba dai, a baya-bayan nan ne Ɗaliban da su ka kammala makarantar a wannan shekara, su ka fito fili tare da bayyana kokensu kan halin da su ka tsinci kansu, sakamakon rashin sakar musu sakamakon.

Ba kuma, abu ne da ya kasance sabo ba, yadda aka saba ganin Ɗalibai na gudanar da bukukuwa da shagulgula iri daban-daban bayan kammala makaranta, sai dai kadhHukumar JAMB ta yi Allah-Wadai Da Matakin Jami’ar Jihar Bauchi, Na Riƙe Sakamakon Ɗalibai

Hukumar shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB), ta bayyana rashin jindaɗinta, kan matakin da Jami’ar Jihar Bauchi, da ke Gadau ta ɗauka, na riƙe sakamakon jarrabawar Ɗaliban da su ka kammala makarantar a wannan shekarar, sakamakon gagarumin bikin nuna farincikin kammala makarantar, da su ka gudanar.

JAMB ta bayyana rashin jindaɗinta game da matakin ne, ta cikin jadawalinta na mako-mako, da ta fitar a ranar Litinin.

Idan ba a manta ba dai, a baya-bayan nan ne Ɗaliban da su ka kammala makarantar a wannan shekara, su ka fito fili tare da bayyana kokensu kan halin da su ka tsinci kansu, sakamakon rashin sakar musu sakamakon.

Ba sabon abu bane ba dai, yadda aka saba ganin Ɗalibai na gudanar da shagulgula, tare da bukukuwa daban-daban, bayan kammala karatunsu na manyan makarantu, sai dai a wannan karon za a iya cewa abin yazo da matsala, bayan da bikin murnar ya jawo hukumar gudanarwar Jami’ar ta ƙanƙanme sakamakon jarrabawar dubban ɗaliban.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button