Ilimi

Jami’a Ta Dakatar Da Malami, Bayan Marin Ɗalibarsa

Jami’ar jihar Imo, da ke birnin Owerri ta dakatar da guda daga cikin Malamanta, Desmond Izunwanne, bisa zarginsa da laifin kwaɗawa wata Ɗaliba mari, bayan da ta makara, kuma ta gaza saka irin kayan da ɗaliban sashen da ta ke karatu ke sakawa.

Ta cikin wani jawabi da mai magana da yawun Jami’ar, Ralph Njokuobi, ya fitar, a Owerri, babban birnin jihar, ya ce Laifin da Malamin ya aikata ba ƙarami bane, kuma abu ne da Jami’ar ba zata lamunta ba.

Jawabin ya kuma ƙara da bayyana cewar, hukumar gudanarwar Jami’ar ta amince da dakatar da Malamin har sai baba ta gani, a ya yin taron gaggawar da ta gudanar.

Kakakin ya kuma ce, an samar da kwamitin ladabtarwa mai ɗauke da mutane uku, wanda zai yi aikin lalubo ire-iren dalilan da ke kaiwa ga aikata irin wannan ɗanyen hukunci, da ma yadda za a kawo ƙarshen ɗabi’ar.

Sanarwar da Jami’ar ta fitar, ta kuma buƙaci al’umma, da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, da su bata lokacin gudanar da bincike, tare da ganin irin hukuncin da za ta ɗauka, akan Malamin.

Wannan mataki kuma, ya zo ne bayan ɓullar wani faifan bidiyo, da ke zagayawa a kafafen sada zumunta na zamani, wanda ke nuna yadda Malamin mai suna, Dr Desmond Izunwanne, na sashen Ilimin Physiology, da ke tsangayar kiwon lafiya, a Jami’ar ta Jihar Imo, da ke Owerri, ya ke hukunta ɗaliban Jami’ar har su huɗu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button