Jami’an Ƴan Sanda Za Su Fuskanci Hukunci, Bisa Rakiya Ga Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai
Rundunar Ƴan Sandan ƙasar nan, ta buƙaci wasu Jami’an ƴan sanda guda biyu da ba a bayyana sunayensu ba, da ke aiki a Ofishin rundunar na Jimeta, jihar Adamawa, da su gurfana a gaban Kwamitin ladabtarwar hukumar, domin fuskantar hukunci, bayan da su ka yi rakiya ga Shugaban ƙungiyar Ɗalibai, a ranakun da ƙungiyar Ɗaliban Jihar Adamawa ta gudanar da zaɓukanta, na 4 da 5 ga watan Satumban da mu ke ciki.
Wani fai-fan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta na zamani, ya nuna yadda Jami’an ƴan sandan masu muƙamin Constables su ke yin rakiya ga Motar sabon Shugaban ƙungiyar Ɗaliban na Katsina.
Sai dai, da ta ke martani kan wannan lamari a ranar Litinin, Helikwatar rundunar ta bayyana cewar, Jami’an ƴan sandan guda biyu sun shallake hurumin da doka ta basu, da ma dalilan aikewa da su zuwa wurin gudanar da zaɓen na ƙungiyar ɗalibai, tare da ƙarawa da bayyana Aikin nasu a matsayin wanda rundunar ƴan sanda ba za ta lamunta ba, domin cin zarafin ayyukanta ne.
Ta cikin jawabin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, a ranar Litinin, Kakakin rundunar ƴan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce an aike da sammaci ga dukkannin Kwastabul ɗin ƴan sandan da ma Jagororinsu, zuwa Helikwatar rundunar, da ke Abuja, domin ɗaukar mataki na gaba.