Jami’an Civil Defence Sun Lakaɗawa Ɗan Jarida Duka, Baya Ga Zargar Kafafen Yaɗa Labarai Da Zama Sanadin Jefa Najeriya Cikin Ƙaƙanikayi
Wasu jami’an hukumar bada kariya ga fararen hula ta ƙasa (NSCDC), sun lakaɗawa wani Ɗan Jarida, mai suna, Izunna Okafor, dukan kawo wuƙa, a jihar Anambra.
Sama da Jami’an hukumar ta Civil Defence 10 ne dai rahotanni su ka tabbatar da cewa, sun rufe Ɗan Jaridar da duka, bisa zargin kafafen yaɗa labarai da zama ummul-aba’isin jefa Najeriya cikin halin ƙaƙanikayin da ta tsinci kanta.
Okafor, wanda wakilin Jaridar 247ureports.com ne, ya je Anambra ɗin ne, daga Nnewi, bayan da aka gayyace shi ɗaukar rahoton gangamin da aka gudanar a Anambra ta Kudu, na Jakadun Soludo, wanda a can ne Jami’an na NSCDC su ka rufar masa.
Rahotanni sun kuma tabbatar da cewar, Ɗan Jaridar ya na cikin motar waɗanda su ka shirya gangamin, wacce ke samun rakiyar Jami’an hukumar ta NSCDC, inda su ka gangara zuwa Awka, wanda a can ne aka gudanar da gangamin, daga bisani kuma aka sake komawa Awka ɗin, a karo na biyu.
Da ya ke mayar da ba’asi a wurin Jami’an tsaro, Ɗan Jaridar ya ce, turka-turkar ta fara ne, a ya yin da ya so sauka daga motar da ya ke ciki, wacce Jami’an na NSCDC ke rufawa baya, a mahaɗar Jami’ar UNIZIK, da ke Awka.
Ɗan Jaridar ya ce, ya fara sanar da Direban Motar ne cewar, ya na son ya sauka a mahaɗar UNIZIK, amma Direban ya banzatar da maganarsa bisa umarnin Jami’an hukumar ta NSCDC, waɗanda su ka ce wajibi ne kowa ya cigaba da zama a cikin motar, har sai anje wurin tsayawar Motoci na ƙarshe, inda su ma za su sauka.
Ya ce, sai da ya ɗaga murya, ya ƙwalla abin da ya ke buƙata da ƙarfi ne, Sannan wasu masu ruwa da tsakin gangamin su ka cewa Direban ya tsaya, domin ya sauka.
Ɗan Jaridar, ya cigaba da cewa, bayan ya sauka ne kuma, sai ya duba ɗaya wayarsa bai ganta ba, ashe ta faɗi a cikin motar ne, ya yin da Direba ya ke ta gaggawar tafiya. Nan da nan kuma ya sanar da su cewar, wayarsa fa ta faɗi a cikin motar, ya na kuma so zai ɗauki abarsa, sai Jami’an Civil Defence ɗin su ka cewa Direban ya tsaya.
Bayan ya miƙa hannu domin karɓar wayartasa daga hannun wanda ya ɗaukota ne kuma, guda daga cikin Jami’an na NSCDC wanda ke aiki da Hukumar Raya Babban Birnin Awka (ACTDA) ya ce wa Direban ya tuƙa Mota su tafi, cikin hanzari kuma su ka rufe ƙofar motar, su ka barshi ɗauke da raunuka a hannunsa.
Haka ya tare motar haya, ya ce ta ajiye shi a wurin da yaji Jami’an sun ce za a tsaya, da zuwansa can ne kuma, ya fara bawa wani Jami’i labarin abin da ya faru, bayan ya tambaye shi abin da ya samar masa da rauni a hannunsa, wanda daga nan ne rikicin ya fara.
Domin kuwa Jami’in ya fara yi masa tsawa ne, nan da nan kuma Abokanan aikinsa su ma su ka fito da bindigu, tare da fara Lissafi daga 11, ai kuwa bai yi wata-wata ba ya ruga a guje, amma su ka kamoshi, su ka fara dukansa da bakin bindiga.
Shigar Daraktan gudanarwar hukumar ACTDA, Mr. Ossy Onuko, cikin lamarin ne kuma, ya sanya lamarin ya lafa, kuma ya ɗauko wayarsa ya damƙa masa, tare da bashi haƙuri, amma har lokacin Jami’an na ta faɗa masa baƙaƙen maganganu, tare da shan alwashin yin maganinsa.
Okafor, ya kuma ce ya shigar da ƙorafinsa ga Jami’in hulɗa da Jama’a na hukumar ta NSCDC, reshen jihar Anambra, Edwin Okadigbo, inda ya yi masa alƙawarin ɗaukar mataki.
Zuwa lokacin da mu ke haɗa wannan rahoto kuma, tuni Babban Kwamandan rundunar na jihar Anambra, Mr. Edwin Osuala, ya bada umarnin zurfafa bincike lamarin.