Ilimi
Jami’ar ABU Ta Lashe Gasar Kimiyyar Abubuwa Masu Rai
Jamiár Ahmadu Bello, da ke Zaria, a jihar Kaduna, ta sake lashe gasar Dalibai ta kasa da kasa, da aka gudanar a Romania.
An kuma gudanar da gasar ne a Jamiár Kimiyyar Abubuwa masu rai, ta Sarki Mihai na I, da ke Timisoara, a kasar Romania.
Jamiár ta Ahmadu Bello, ta kuma samu wakilcin, Abubakar Ahmed, Aminu Abubakar Sadiq, da Zakariyya Saminu ne, wadanda dukka suka fito, daga tsangayar koyon Aikin noma.
An kuma bayyana tawagar ta Jamiár Ahmadu Bello ne, a matsayin wadanda su ka yi nasara a kashi na shida na gasar, wacce aka gudanar kan fannonin Kimiyyar Halittu Masu Rai Da Noma.
Bayanin hakan kuma, ya fito ne ta cikin wani jawabi, da Daraktan sashen hulda da jamaá, na Ofishin shugaban Jamiár, ya fitar a jiya.