Jami’ar Aliko Ɗangote, da ke Wudil Ta Fitar Da Cut-Off, Tare Da Fara Rijistar Post-UTME
Jami’ar Aliko Ɗangote, da ke garin Wudil a Jihar Kano, ta amince da maki 160 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga Jami’ar.
An kuma fara rijistar Post-UTME daga yau (Litinin), 11 ga watan Satumba, zuwa ranar 24 ga watan na Satumban 2023.
Bayanin hakan kuma, na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa da Magatakardan Jami’ar, Dr. Naheed Ibrahim ya sanyawa hannu, wacce ta bayyana cewar wajibi ne ga dukkannin ɗalibin da zai nemi gurbin karatu a Jami’ar, ya sanyata a matsayin zaɓinsa na farko (First Choice), tare da samun mafi ƙarancin makin da bai gaza 160 ba.
KU SANI : Akwai kwasa-kwasan da ake buƙatar maki 180, irinsu BSc. Architecture, BSc. Biochemistry, BSc. Biology, BSc. Computer Science, B.Eng. Civil, B.Eng. Electrical, BSc. Information & Communication Technology, B.Eng. Mechanical, da BSc. Microbiology, da BSc. Science Laboratory Technology.