JAMI’AR BAYERO TA BUƊE SHAFIN RIJISTAR POST-UTME DA ONLINE SCREENING
Jami’ar Bayero, da ke birnin Kano, ta amince da maki 180 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga Jami’ar ga ɗaliban da su ka rubuta jarrabawar JAMB ta shekarar 2023/2024, tare da sanya Jami’ar a matsayin zaɓinsu na farko (First Choice).
Haka zalika ta buɗe shafin rijistar POST-UTME, da Online Screening (Ga Ɗaliban DE), a ranar Litinin 20 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, ana kuma sa ran rufewa a ranar Lahadi, 7 ga watan Janairun 2024.
YADDA AKE RIJISTA:
•Ɗaliban UTME za su halarci Adireshin makarantar akan: https://buk.edu.ng, sannan su danna maɓullin ‘2023 UTME ONLINE SCREENING EXERCISE’.
• Sai su shiga Profile ɗinsu, ta hanyar amfani da JAMB Registration Number a matsayin Username, sai makin da su ka samu a jarrabawar UTME a matsayin Password.
•Bayan ya buɗe, sai su cike dukkannin bayanan da ake buƙata, sannan hoton da aka ɗauke su, a ya yin rijistar JAMB zai bayyana.
•Sai su yi Generating ɗin PPI, su kuma yi amfani da RRR ɗin da ke jiki, wajen biyan Naira 2,000 kuɗin Post-UTME (Ɗalibai su na da zaɓin biya da katinansu ta Online, Internet Banking, ko kuma ta hanyar biya a bankuna).
•Bayan ɗalibi ya biya kuɗinsa, sai ya koma shafin makarantar ya cire Acknowledgement Slip (Za a cigaba da cire Slip, har zuwa tsakar daren Lahadi, 14 ga watan Janairun 2024).
Ku Sani : Za a sanar da ɗalibai wuri, da lokacin da za su rubuta jarrabawarsu ta Post-UTME, ta hanyar lambar waya ko Adireshin Email ɗin da su ka bayar, a ya yin rijistar ta Post-UTME.
Ɗaliban da ke da lalurar gani, ko waɗanda za su zo daga ƙasashen ƙetare, ba za su rubuta jarrabawar POST-UTME ba, kawai za su yi rijista ne.
√• Ɗaliban DE, za su yi rijista ne, ta Adireshin: https://mybuk2.buk.edu.ng/bukdes/, Kuma za su yi amfani da DE Number da State ɗinsu domin Login.
✍️ MIFTAHU AHMAD PANDA
08039411956