Jami’ar Jihar Gombe Ta Sanya Lokacin Buɗe Shafin Rijistar Post-UTME
Jami’ar Jihar Gombe (GSU) ta sanya ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, a Matsayin ranar da za ta buɗe shafinta, domin fara rijistar Post-UTME ga Ɗaliban da su ka sanyata a matsayin zaɓukansu na farko (First Choices) a kakar karatu ta 2023/2024.
Jami’ar ta kuma amince da maki 150 a matsayin mafi ƙarancin makin da ake buƙatar Ɗaliban da su ke nemanta su rabauta da shi a jarrabawar JAMB UTME.
Haka zalika, wajibi ne, waɗanda ke neman gurbin karatu a sashen Likitanci (Medicine), Ilimin haɗa magunguna (Pharmacy), da fannonin Shari’a (Law), su samu aƙalla maki 200.
Ɗaliban da su ka nemi MBBS, kuma makinsu bai kai 200 ba, Jami’ar ta shawarcesu da su canja Course zuwa, B.N.Sc Nursing, B.Sc Human Nutrition and Dietetics, B.Sc Public Health, B.Sc Environmental Chemistry & Toxicology, B.Sc Biotechnology, B.Sc Pharmacology, da B.Sc Industrial Chemistry.
Haka zalika, waɗanda su ka nemi Law, kuma makinsu bai kai 200 ba, su ma za su iya sauya Course zuwa: B.LIS Library and Information Science, B.Ed Educational Management, B.Sc Banking & Finance, B.Sc International Relation, ko B.Sc Peace and Conflict Resolution.
Haka zalika su ma ɗaliban da ke neman DE da NCE, IJMB, ko Diploma, wajibi ne ya kasance abin da su ka nema, shi ne wanda su ka karanta a matakin da su ka kammala.
Ɗaliban da su ka cika sharuɗɗan da mu ka lissafa a sama, za su yi rijistar Post-UTME ne, tare da biyan Naira 2,000 kuɗin rijista.
MATAKAN RIJISTAR:
•Ɗalibi zai shiga adireshin: https://dnrd-gsu-edu.com/admission, akan browser ɗinsa.
•Sai ya saka JAMB Registration Number ɗinsa, ya kuma danna ‘Get Details’.
•Sannan zai biya kuɗin rijistar a Online ta hanyar katin ATM, ko Taransifar Banki.
•Daga nan zai koma shafin ya cike sauran bayanansa, ya kuma taɓa maɓullin ‘Register’.
•Dukkannin bayanan da ya saka, za su bayyana, sai ya danna ‘Generate Data Form’.
•Zai ga PDF mai feji biyu ya yi Download akan Computer ko Wayarsa.
_Shikenan ya kammala rijista.
√• Feji na farko ya na ɗauke da bayanan rijistar Ɗalibi ne.
√• Shi kuma feji na biyu shi ne Exam Card ɗinsa.
KU SANI: Za ku yi Printing ɗin dukkannin Pages biyun, ku kuma yi Photocopy ɗinsu, tare da sauran takardunku, sannan ku tafi da su Department ɗin da ku ka nema, ya yin tantancewar Ido da Ido (Physical Screening).
✍️MIFTAHU AHMAD PANDA
08039411956