Jami’ar Jihar Yobe (YSU) Ta Fitar Da Cut-Off Mark
Jami’ar jihar Yobe, da ke birnin Damaturu, ta amince da maki 140 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga Jami’ar, ga Ɗaliban da ke neman makarantar da jarrabawar JAMB UTME.
Ta kuma sanya ranar Alhamis, 21 ga watan Satumban da mu ke ciki, a matsayin ranar fara rijistar Post-UTME, da Online Screening (Ga Ɗaliban DE), inda aka shirya rufewa, a ranar 12 ga watan Oktoba.
Bayanin hakan na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa da Jami’ar ta fitar, mai ɗauke da kwanan watan Laraba, 20 ga watan Satumban 2023.
Sanarwar ta kuma bayyana cewar, Wajibi dukkannin Ɗalibin da ke neman gurbin karatu a sashen Physiotherapy ya samu maki aƙalla 190; 170 ga masu Anatomy; 170 ga Physiology; 180 ga Law; Biochemistry – Geology – Microbiology – Da Biology dukka 150; Computer Science 170; sai kuma Public Administration & Sociology da ake buƙatar maki 150.
Ɗalibai za su iya rijistarsu ta Post-UTME, ta adireshin: https://ysu.edu.ng/putme, tare da biyan Naira 2,000 a matsayin kuɗin rijista.